Assalamu alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh
Muna Maraba daku A Shirin Akademiyyatu Manasik Na Ilmantar Da Aikin Haji
Muna Gode Maku Bisa Nuna Yardarku Damu Da Gudumowarku Da Bibiyar Da Kuke Yiwa ayyukanmu. Kuma Muna yi maku fatan amfana da lokutanku wajen sanin ilmomin ibadar aikin haji da umara da ziyara.Flag Arabic

Makarantar Manasik

Tsarin Akademiyyatu Manasik na koyarwa ta hanyar Na'ura Mai kwakwalwa, wani budadden minbari ne ga kowa don karatu da bita a fannin ilimin Shari'ah, wanda Ma'aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci Da Da'wah Da Shiryarwa ta Kasar Saudi Arabiya Ta Shirya.

A fitowar sa farko wannan minbari zai bayyana a harsuna takwas (Larabci – Turanci – Turkiyyanci – Indonisiyyanci – Hausa – Faransanci – Urdu – Bangladesh). Za a ci gaba da kara wasu harsunan lokaci-zuwa-lokaci.

Ma'aikatar Harkokin Addinin Musulunci ita ce ta tsara kuma ta gudanar da bitar wadannan darussa baki-daya kuma an barsu kyauta ga dukkan mambobi ba tare da biyan ko kwabo ba.

Duk mai bukatar fa'idantuwa da wannan manhajar karatu da bita lallai ya zama kafin hakan yayi rajista. A karshen kowane zango za ayi wata takaitacciyar jarabawa kan karatun da aka yi. Wanda ya ci nasara a wannan jarabawa zai samu shaidar kammalawa.

WASU DAGA CIKIN DARUSSAN

Ziyarar Masallacin Manzo (S.A.W.)
5 Darussa
Ina Shaidar Daku Cewa Na Gafarta Musu
5 Darussa
Ihrami
5 Darussa

AMFANI DA MANHAJOJIN WAYAR HANU

Ta Hanyar amfani da manhajojin wayar hanu za ka iya halartar wannan bita cikin matukar sauki kuma bisa tsarin da ba shi da bambanci da tsarin da ke kan intanet a kwamfuta.

 • Bayanin Mai Girma Ministan Harkokin Addinin Musulunci Da Da'wah Da Shiryarwa

  Yabo da godiya su tabbata ga Allah. Salatin Allah da AmincinSa su tabbata ga Annabinmu Muhammadu da Iyalen gidansa da Sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ta’ala ya yiwa Ma’aikatar Kula da Al’amuran Addinin Musulunci Da Da’wah Da Nusarwa dacewa da gam-da-katar wajen amfani da tsare-tsare dabam-daban na zamani don bayanin ilimomin ibadar aikin haji, kuma ta hanyoyi da harsuna mabambanta. Wannan shiri na Akademiyyatu Manasik wanda aka kebance shi don yada ilimomi da hukunce-hukuncen ibadar aikin Haji da Umara da Ziyara daya ne daga cikin sabin tsare-tsare na fasahar zamani wadanda manufar fito dasu ita ce karfafa fadin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam: ((Ku riki iliminku na ibadar Haji daga gare ni)). Kuma lallai wannan Makaranta za ta bada gudumowarta wajen saukaka wadannan ilimomi a takaice kuma yadda za a fahimce su, kamar yadda za ta yi kokari wajen sanya ilimomin cikin saukin da Alhazai za su iya karatun daga gidajensu a kasashensu, ta hanyar fasahar zamani da tsare-tsare dabam-daban na sadarwar zamani, domin a dama da ita, kuma ta dace da cigaban zamanin da yake aukuwa da gaggawa a duniyar fasaha. Kamar yadda za ta isar da ilimomin domin saukake ayyukan wayarwa da nusarwa ta yadda zai dace da kwadayin da Shugabannin wannan kasa suke da shi da kuma kudurinsu da hangensu na ganin an samu cigaba a irin hidimar da ake yiwa Alhazai da masu Umara ta hanyar amfani da tsare-tsare masu yawa na fasahar zamani. Muna rokon Allah Ta’ala Ya saukakewa Alhazai gudanar da wannan farilla tasu, kuma Ya taimaki cibiyoyi da bangarorin da suke da ruwa-da-tsaki ta hanyar basu dacewa cikin yin ayyukan da aka dora musu daidai da umarnin Mai Hidima Ga Masallatai Biyu da kuma Mai Jiran-Gadonsa, “Allah ya karfafesu baki daya”.

  Salih ibn Abdul'Aziz ibn Muhammad Al al-Shaikh
 • Bayanin Mai Girma Mataimakin Minista Mai Kula Da Harkokin Masallatai da Da'wah da Shiryarwa

  Muna maraba daku a wannan tsari na "Akademiyyatu Manasik" wanda ta hanyarsa muke gabatar da hidima a fagen aikin wayar-da-kai da sabon salo, domin Musulmi a kowace nahiya ta duniya su samu damar sanin ilmomin aikin Haji da sauran ilmomin shari'ah masu alaka da tafiya Haji. Wasu fitattun malamai ne daga cikin masu aikin wayar-da-kai a Haji da Umara da ziyara suka tsara kuma suka gudanar, bisa ma'aunai madaukaka na ilimi da fasahar kwarewa mai matukar kyau. Muna rokon Allah Ta'ala ya bada dacewa ga 'yan uwan da suka gabatar da wannan aiki, kuma ya taimakesu. Kamar yadda muke mika godiya ga dukkan malaman da suka bada gudumowarsu a wannan sabon tsari, tare da fatan ci gaba da samun karfafawa da taimakawa daga kowa da kowa wajen sanarwa da yada wannan sabuwar fasahar yada ilimi. Da fatan za a nemi saduwa da wannan Ma'aikata don neman bada dukkan shawarwari da kuma tabbatar da habaka wannan tsari.

  Dr. Taufiq ibn Abdul'Aziz al-Sudairi

Biyan kuɗi zuwa da aikawasiku jerin

Abubuwan Da Wannan Manhaja Tayi Fice Da shi

 • Kayan karatun na musamman ne don wannan tsari kuma amintattu ne

  Mazartar da aka samo wannan karatu masu Magana akan ibadar aikin Haji an rubuta su ne don wannan tsari kadai, kuma amintattu ne wadanda sanannu kuma yardaddun malamai suka duba suka amince da su.

 • Dukkan abin kyauta ne

  Rajista da kuma dukkan kayan ilimi da ilmantarwa da jarabawa da shaidar halarta duk kyauta ne babu biya

 • Dukkanin Manhajojin Da aka Sanya Wannan Bita Cikinsu Suna Aiki

  Za ka iya farawa kuma ka kamala bitarka ta hanyar dukkan minbarorin ko manhajojin da aka sanya wannan karatu (wato Wayar Hannu; Na'urar Allon Talla; Yanar Gizo; Na'urar Hidima Ta Latsa-Da-Kanka)

 • Harsuna Dabam-daban

  Ana gabatar da darussan wannan tsari da manhajoji ne cikin harsuna takwas ya zuwa yanzu

 • Lokutan karatun Zabi-da-kanka ne

  A kowa ce rana da kowa ne lokaci, ko da safe ko da yamma, za ka iya yin rajista halarta kuma ka fara wannan karatu da bita.

Partners

Bugawa News