Assalamu alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh
Muna Maraba daku A Shirin Akademiyyatu Manasik Na Ilmantar Da Aikin Haji
Muna Gode Maku Bisa Nuna Yardarku Damu Da Gudumowarku Da Bibiyar Da Kuke Yiwa ayyukanmu. Kuma Muna yi maku fatan amfana da lokutanku wajen sanin ilmomin ibadar aikin haji da umara da ziyara. Flag Arabic Flag Arabic

Makarantar Manasik

Tsarin Akademiyyatu Manasik na koyarwa ta hanyar Na'ura Mai kwakwalwa, wani budadden minbari ne ga kowa don karatu da bita a fannin ilimin Shari'ah, wanda Ma'aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci Da Da'wah Da Shiryarwa ta Kasar Saudi Arabiya Ta Shirya.

A fitowar sa farko wannan minbari zai bayyana a harsuna takwas (Larabci – Turanci – Turkiyyanci – Indonisiyyanci – Hausa – Faransanci – Urdu – Bangladesh). Za a ci gaba da kara wasu harsunan lokaci-zuwa-lokaci.

Ma'aikatar Harkokin Addinin Musulunci ita ce ta tsara kuma ta gudanar da bitar wadannan darussa baki-daya kuma an barsu kyauta ga dukkan mambobi ba tare da biyan ko kwabo ba.

Duk mai bukatar fa'idantuwa da wannan manhajar karatu da bita lallai ya zama kafin hakan yayi rajista. A karshen kowane zango za ayi wata takaitacciyar jarabawa kan karatun da aka yi. Wanda ya ci nasara a wannan jarabawa zai samu shaidar kammalawa.

WASU DAGA CIKIN DARUSSAN

Rukunan Musulunci
5 Darussa
Girmama Gari Mai Alfarma
5 Darussa
Manufofin Haji A Kur'ani
5 Darussa

AMFANI DA MANHAJOJIN WAYAR HANU

Ta Hanyar amfani da manhajojin wayar hanu za ka iya halartar wannan bita cikin matukar sauki kuma bisa tsarin da ba shi da bambanci da tsarin da ke kan intanet a kwamfuta.

Biyan kuɗi zuwa da aikawasiku jerin

Abubuwan Da Wannan Manhaja Tayi Fice Da shi

 • Kayan karatun na musamman ne don wannan tsari kuma amintattu ne

  Mazartar da aka samo wannan karatu masu Magana akan ibadar aikin Haji an rubuta su ne don wannan tsari kadai, kuma amintattu ne wadanda sanannu kuma yardaddun malamai suka duba suka amince da su.

 • Dukkan abin kyauta ne

  Rajista da kuma dukkan kayan ilimi da ilmantarwa da jarabawa da shaidar halarta duk kyauta ne babu biya

 • Dukkanin Manhajojin Da aka Sanya Wannan Bita Cikinsu Suna Aiki

  Za ka iya farawa kuma ka kamala bitarka ta hanyar dukkan minbarorin ko manhajojin da aka sanya wannan karatu (wato Wayar Hannu; Na'urar Allon Talla; Yanar Gizo; Na'urar Hidima Ta Latsa-Da-Kanka)

 • Harsuna Dabam-daban

  Ana gabatar da darussan wannan tsari da manhajoji ne cikin harsuna takwas ya zuwa yanzu

 • Lokutan karatun Zabi-da-kanka ne

  A kowa ce rana da kowa ne lokaci, ko da safe ko da yamma, za ka iya yin rajista halarta kuma ka fara wannan karatu da bita.

Partners

Bugawa News