Background Image

Game The Academy

 • Burinmu

  Bayar da gudumowa wajen habaka aikin wayar-da-kan alhazai da masu umara, kuma don wannan aikin fadakarwa ya zama ba bayyane kuma ana yin ta a kowane lokaci, ta hanyoyin sadarwa na zamani, da manhajojin fasahar zamani ta hanyoyi dabam-daban da kuma sababbin salo-salo da harsuna dabam-daban.

   

  Sakonmu

  Muna kokarin isar da sakonmu zuwa ga gwargwadon yankin da zamu iya isa gareshi na mutanen da suke kwadayin sanin ilimin aikin haji, kuma mu yi bayanin hukunce-hukuncen aikin haji da umara da wajibansu ta hanyoyin sadarwa na zamani kuma cikin harsuna dabam-daban wanda gudanar ta hanyar ma'aikatanmu na aikin wayar-da-kai a haji da umara da ziyara.

   

  Manufarmu

  -  Sharhin rukunan Musulunci guda biyar tare da mai-da-hankali akan rukuni na biyar

  -  Yada ilmomi da kuma hukunce-hukuncen Haji da Umara

  -  Karfafa matsayi da darajar garin Makka

  -  Dasa manufofin tsakaituwa da daidaituwa

  -  Karfafa manufar saukakawa a hukunce-hukuncen aikin Haji

  -  Karfafa manufar girmama tsari da bin doka

  -  Amfani da fasahar zamani wajen sharhin ilmomin aikin Haji