Background Image

Labaranmu

SABUWAR MAHANGA GAME DA SHARHI AKAN AIKIN HAJI

SABUWAR MAHANGA GAME DA SHARHI AKAN AIKIN HAJI

3:25 am Friday 5th Dhu al-Qi'dah 1438 H

Babban Shehin malami kuma Mai bada shawara ta musamman ga Ministan Sha’anin Addinin Musulunci, da Da’awa da Nusantarwa, Sheikh Xalal Ibn Ahmad al-AQeel ya bayyana cewa: “Lallai tunanin Akadimiyar Manasik ta samu asali ne daga mahangar mai girma Ministan Sha’anin Addinin Musulunci da Da’awa da Nusarwa (wato) Shaikh Salih Ibn Abdul 'Aziz Ibn Muhammad Aal-Shaikh. Wanda yake nuna wajibcin bunqasa duk ayyukan wannan ma’aikata gaba daya da kuma wayar da kan mahajjata a kevance.

     Haqiqa wannan mahanga ta ribatu matuka ta hanyar samun kulawa ta musamman daga mai girma mataimakin minista Dakta Taufiq Ibn Abdulaziz As-Sudairi wanda ya nuna wajibcin tsayuwar daka da tabbatuwa akan wadannan sababbin hanyoyin yaxa ilimomi, daga cikin su harda hanyar ilmantarwa daga nesa.

     Kuma haqiqa aikace-aikacen Akadimiyar Manasik sun samu asali ne daga wannan umurnin. A karon farko Akadimiyar Manasik ta fitar da (shirye shiryenta) ne da yarurruka guda takwas masu muhimmanci ta hanyar dogaro da kididdigen yawa da aka yi ahukumance, domin Akadimiyar Manasik ta zamo matashi na karantarwa da wayarwa da aka keve domin wayar da kan mahajjata da yaxa ilimin aikin haji ta hanyar amfani da na’ura (na zamani) da qirqire-qirqire, da kuma qwarewa wajen sharhi da bayani game da ilimin aikin hajji domin  taimakawa wajen qarfafa ilimi da yada koyarwa da bayyanawa da nusantarwa wanda ya shafi aikin haji da hukunce-hukunce game da rukunin nan na biyar.

Kuma domin aikace-aikacen Akadimiyar Manasik su yalwata ga mahajjata da masu umara ta hanyar basu isashshen lokaci tsawon shekara ta yadda mahajjatan na cikin gida dana waje da duk yan kasa da mazauna kasa dama masu kwadayi su amfana wajen sanin hukunce-hukuncen aikin hajji da umara da ziyara a kasashe daban-daban na duniya ta hanyar kafofin sadarwa, da yanar gizo da wayoyin hannu masu kwakwalwa da komputa da alluna na zamani.

   Kuma Al-AQil ya miqa godiya ta musamman ga ma’abota daraja malaman da’awa wadanda suka taimaka wajen gabatar da ilimi da darussa, kuma sune wadannan manyan maluman da suka kware wajen wayar da kan alhazai wanda kuma suna da masaniya mai yalwa wajen sharhin ilimin shari’ah da ilimantarwa a makarantu.

   Kuma suna daga cikin tatattun malamai masu wayar da kai akan aikin Haji da Umara da Ziyara, kuma sun yi fice wajen da’awa da wayar da kan alhazai da masu Umara da masu ziyara a kasar Saudiya, tare da su akwai maluma masu da’awa  a wasu qasashen a qarkashin ma’aikatar addinin Musulci, kuma qwararru daga cikin waxanda su ka yi karatu a jami’oin qasar Saudiya kuma suka samu shaidar kammala karatu a fannonin shari’a da aqida da fiqihu, suma sun yin tarayya a wannan aikin.