Background Image

Labaranmu

TSARE TSAREN KOYADDA AIKIN HAJJI DA ABUBUWAN DA ZASU KAWO NASARA

TSARE TSAREN KOYADDA AIKIN HAJJI DA ABUBUWAN DA ZASU KAWO NASARA

3:25 am Friday 5th Dhu al-Qi'dah 1438 H

Shugaban Akadimiyar Manasik mai zartarwa mai suna shaikh Xalal Ibn Ahmad Al-Aqil ya bayyana cewa: Akadimiyar Manasik ta samu tallafi cikakke daga mai martaba wazirin al-amuran musulunci da da’awa Shaikh Salih Ibn Abdulaziz Ibn Muhammad aal-al-Shaikh, hakanan daga wajen mai Martaba Mataimakin wazirin vangaren lura da al-amuran masallatai da da’awa da nusantarwa mai suna Dakta Taufiq Ibn Abdulaziz As-Sudairi, yana mai qarfafa cewa, shi waziri ya bada umarni a gaggauta bawa Akadimiyar Manasik abin da take bukata domin hidindimun Akadimiyar su fara fita da wuri, da yarurrukan da ake buqata, domin wannan aikin (Akadimiyar Manasik) ya wayi gari shine nau’i na farko, da a ka keve domin sharhin ilimin aikin Haji da yada dukkan sanarwa da nusantarwa game da aikin haji da hukunce-hukuncensa umara da ziyara, domin gabatar da shirye shirye wa alhazai da masu umara da sauransu daga cikin waxanda ke son samun masaniya dangane da rukuninnan na biyar (aikin haji) daga sassan duniya daban-daban da qasashen Musulunci ta hanyar yanar gizo kuma ta hanyar kwamputoci da na’urori daban-daban.

Haqiqa waxanda suka yi tarayya wajen gabatar waxannan darrusan wasu zavavvun malumane kuma gogaggune a wannan fagen na ilimin addini, wasunsu suna cikin qasar  Saudiyya wasu kuma suna wajenta wadanda suma a jami’oin Saudiyya suka yi karatun addini. Yawan maluman ya wuce arba’in, sun bada gudunmawa wajen shirya darrusa a talabijin fiye da dubu cikin yarurruka guda takwas daga cikin yarurrukan duniya,dag cikinshirye shiryen da ma’aikatar addinin Musulunci ta Saudiyya ta ke gabatarwa domin karantar da Musulmai hanya ingantacciya wacce ta dace Sunnar Annabta game da wannan tafiyar mai albarka.      

Mai bawa ministan al-amuran addinin Musulunci mai suna Shaikh Xalal Ibn al-Aqil ya ce: Muassasar Hasan Abbas Sharbatli ta ayyukan alkhairi ta bada gudunmawa ga wannan tafiyar, ita wannan mu’assar xaya ce daga cikin muassasosi na cikin gida Saudiyya da ke tallafawa al-amuran da’awa sosai.

Al-Aqil ya miqa godiyarsa zuwa ga shugaba muassar da jagororinta saboda taimako akai-akai da suke bawa ma’aikatar aikin addinin Musulunci, ya kuma yaba matuqa wa shugaban mu’assasar mai zartarwa wato Ustaz Adbullaxif Al-Naqli. 

Al-Aqil ya kamala maganarsa da cewa aiki da jama’a ya na da tasirin gaske da kuma sakamako mai kyau – tare da cewa Ma’aikatar al-amuran addinin Musulunci – suna karfafa aikin hadakaka da tafiya tare domin cimma maunafar aikin da’awa da ingantashi da yada ma’anonin AlQur’ani Mai Girma da Sunnar Annabi -Tsira da aminci su tabbata agareshi- domin qarfafa tushen ilim shari’a da manufofinta da sirar Annabi - Tsira da aminci su tabbata agareshi-   ta kafofi na zamani da yarurrukan duniya da karfafa tsakatsaki da daidaituwa a tsakanin Musulmai da ma’anar tausayawa juna da taimakawa juna da }aunar juna da ha]in kai da kyawawan xabi’u da kyawawan halaye.