Background Image

Labaranmu

MANASIK ITACE TSANGAYA TA FARKO KEVANTACCIYA DOMIN KARANTAR DA AIKIN HAJI DAGA NESA

MANASIK ITACE TSANGAYA TA FARKO KEVANTACCIYA DOMIN KARANTAR DA AIKIN HAJI DAGA NESA

3:25 am Friday 5th Dhu al-Qi'dah 1438 H

Shugaban Mai Zartarwa na Manasik Shaikh Xalal Ibn Ahmad Al-Aqil ya bayyana cewa tsangayar Manasik (Akadimiyar Manasik) daya ce daga cikin ayyukan na’ura mai qwaqwalwa na Ma’aikatar Al-amuran Addinin Musulnci da Da’awa da Nusarwa da ke Masarautar Kasar Saudiya. Ya tabbatar da cewa aikin karantarwa ne da wayar da kai ta hanyar na’ura, wanda zai taimaka wajen yaxa ilimin aikin Haji da Umara da Ziyara a qasashe dabam-daban na Musulunci ta hanyar yanar-gizo.

Tsangayar Manasik (Akadimiyar Manasik) zagaye ne daga cikin hidimomin shirye shiryen da Ma’aikatar Al-amuran Addinin Musulunci ke gabatarwa domin karantar da Musulmai tafarki mai inganci wanda ya dace da tafarkin Annabci na wannan tafiyar mai albarka (Haji da Umara, da Ziyara).

Mai bawa wazirin ma-aikatar al-amuran addinin Musulunci shawar wato Shaikh Xalal al-Aqil ya sanar da cewa Akadimiyar Manasik zata kasance zance-duniya kasancewarta tsangaya ta farko ta karantarwa, dake nufin duk masu burin sanin aikin haji a duniya, musamman masu son su amfana da wannan hidimar ta kyauta, wacce ta ke gabatar da darrusa da harsuna guda takwas, wanda zavavvu daga cikin masu kira domin wayar da kai a aikin Haji da Umara da Ziyara, wadanda amintattu ne game da wannan aikin daga cikin qwararrun maluma da masana suka gudanar.

Al-Aqil ya tabbatar da cewa Akadimiyyar Manasik zata fara gudanar da shirye shiryenta satin farko awatan Zulqa’dah, shekarar 1438 Hijira. Domin baqin Allah Mai Rahama su amfana da karatuttukan a lokacin aikin haji mai gabatowa.

Ya tabbatar da cewa Akadimiyyar Manasik ta na tafe ne karkashin kulawar Mai Hidima Ga Haramaini masu daraja wato Sarki Salman Ibn Abdulaziz aal-Su’ud da Mai Martaba Mai jiran gadonsa dai dai da abin da ya dace da mahangar masarauta ta 2030.

Ya yi nuni cewa Akadimiyyar Manasik a matakinta na farko zata karantar da aikin Haji da yaruka na tushe, sa’annan za ta faxaxa har ta kai ga samar da hidima cikin yarurrukan duniya.

Al-Aqil ya jaddada cewa Ma’aikatar Addinin Musulunci ta hanyar qwararru masana na’ura da malamai sun yi aiki tare tukuru domin sanya tushen wannan shirin, kuma sun daura wa gwanaye a wannan fagen nauyin, kuma Akadimiyar Manasik ta maida hankali zuwa ga sabon salo tare da bambantawa da horaswa da yin amfani da tsare tsare na karantarwa da na’ura domin cimma burin Ma’aikatar Al’amuran Addinin Musulunci na isar da sakonni da ilimantarwa ta hanyar kafofi na zamani da yarurruka dabamdaban da daukan hakan akan babban manufa na dukkan ayyukan Akadimiyyar Manasik.

Ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Addinin Musulunci ta maida hankalinta a Akadimiyyar Manasik akan mahangar son aiki tare, wato haxaka da binciken hanya mafi sauki domin karantarwa, da nufin yaxa karatu mai inganci a taqaice kuma a sawwaqe, ta yadda za a yi saurin ganewa da fahimta, domin sharhin shikashikan Musulunci da bayyana farillan aikin haji, hakan zai samu ne ta hanyar karfafa kwazo, da inganta shirye shirye, da kyautata kayan aiki, da bambanta kafofin horaswa.

Ya bayyana cewa aiwatar da aikin Akadimiyyar Manasik ya zo ne ta hanyoyi da jerin shirye shirye  matsakaita wanda aka gina akan tsarin aiki mai girma, mai gamsarwa, na nuna kwazon Masarautar Kasar Saudi Arabiya wajen samar da dukkan abun bukata mai yiwuwa domin hidimar bakin Allah mai Rahama daidai da abinda Shuwagabanni shiryayyu ke tsinkaye tare da bayyana cewa Akadimiyyar Manasik zata yi aiki da tsari na dan lokaci domin karantar da masu amfana da shirye shiryenta tushen aikin Haji daidai da karantarwar Alkur’ani da Sunna tare da lura da karfafa manufar tsakatsaki da daidaituwa da hurumin lokaci da bigire da abinda yake da dangantaka da wajibai da shikashikai na hukunce hukuncen shari’a. Shaikh Xalal Al-Aqil ya fayyace manufofin Akadimiyyar Manasik waxanda suka kunshi yaxa wayewa da ilimi da hukunce hukuncen manasik (aikin haji da Umara) ta matakai kamar haka

  • Sharhin aikin Haji da Umara da Ziyara a bisa tafarkin magabata managarta da malumanmu masu daraja.
  • Amfani da kafofi da hanyoyin sanarwa da yada labarai domin yin sharhi da sawwaka ilimin manasik (aikin Haji da Umara) da yarurruka masu yawan adadi.
  • Sharhin manufa da ma’anonin rukunan Musulunci, da shikashikan Imani da ihsani da xabi’u da halaye da tarihin Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- da ilimummukan da suka shafi AlQur’ani Mai Girma da bayyana su ta hanyar taron-qarin ilimi da shirye shirye na talabijin na kallo da sauti da karatu.

Ya bayyana hangensa na cewa Akadimiyyar Manasik zata  kasance daya daga cikin kafofin karantarwa mai tasiri wanda zata taka rawar gani wajen yada karatuttuka da ilimi wanda yake hade da aikin Haji da Umara da Rukunansu da wajibansu da hukunce hukuncensu da hukunce hukuncen Aqida da shari’a wa baqin Allah mai Rahama da qoqari domin hutawarsu da kwanciyar hankalinsu da amincinsu da kulawa da su ta hanyar nusar dasu da wayar musu da kai.

Shaikh Al-Aqil mai bawa ministan Ma’aikatar Al-amuran Addinin Musulunci da Da’awa da Nusarwa na sha’anin aikin Haji da Umara da kafofin yada labarai, ya tabbatar da cewa Akadimiyyar Manasik zata gabatar da hidimomi ta kafar “Wasa’id al-Manasik” na kyauta cikin shirye shiryenta na kulawa da karfafa ganawa da mafiya yawa daga cikin alhazai kuma da kokari domin tabbatar da yaxuwa da amfanuwa da kafofin sadarwa na zamani domin wayarwa ta hanyar waya da na’urar komputa da allo na na’ura, ba tare da lura da inda mutum yake ba.  Yarukan da wannan tsari ya shafa har zuwa yanzu sune Larabci, Turanci, Turkanci, da harshen Indunisiya da Hausa da Sawahili da Urdu da Bangaliya.